IHR ta buƙaci hukumomin Hajji na jihohi da su wayar da kan maniyyata game da taƙaitaccen lokacin rijistar Hajji - Hajj News

Header Ads

Header ADS

IHR ta buƙaci hukumomin Hajji na jihohi da su wayar da kan maniyyata game da taƙaitaccen lokacin rijistar Hajji

IHR ta buƙaci hukumomin Hajji na jihohi da su wayar da kan maniyyata game da taƙaitaccen lokacin rijistar Hajji
IHR ta buƙaci hukumomin Hajji na jihohi da su wayar da kan maniyyata game da taƙaitaccen lokacin rijistar Hajji

Independent Hajj Reporters, IHR, ƙungiya mai zaman kanta da ta shahara wajen kawo rahotanni kan aikin Hajji da Umara a Nijeriya da ƙasashen waje, ta yi kira ga Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da hukumomin Hajji na jihohi da kamfanonin Hajji masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki da su fara gudanar da shirye-shiryen wayar da kai da ilimantar da maniyyatan Hajjin 2024 a Najeriya game da taƙaitaccen lokacin yin rijista da ake da shi.

IHR ta ce akwai buƙatar a faɗakar da maniyyatan Najeriya masu burin sauke farali a 2024 cewa, cewa an wuce lokacin da maniyyata za su ki yin rijista har sai ya rage 'yan kwanaki kafin fara jigilar maniyyata.

A cewar sanarwar da kodinetan IHR na kasa, Ibrahim Muhammad ya fitar, wannan kira ya zama wajibi sakamakon kiraye-kirayen da ƙungiyar ke samu kulli yaumi daga musulmin Najeriya, waɗanda ke neman sanin ko an fara rijista a jihohinsu.

Wanda hakan ke nuni hukumomin alhazai na jihohi ba sa wayar da kan al'umma game da irin illar da ke tattare da jinkirin yin rijista.

Ya zuwa yau, kwanaki 140 suka rage kafin buɗe shafin neman biza don Hajjin 2024 ga maniyyata Hajjin bana, yayin da ya rage kwanaki 250 kafin rufe bayar da biza. A nata ɓangaren, ya zuwa 1 ga watan Maris, 2024, Saudiyya za ta fara bayar da biza sannan ta rufe bayarwa ran 29 ga Afrilun 2024. 

Bugu-da-ƙari, Ma'aikatar Hajji da Umara ta Saudiyya ta bai wa hukumomin Hajji ciki har da NAHCON, umarni a kan a kammala bada aikin tanadin masauki da Masha’er kada ya wuce 25 ga Fabrairu, 2024.

Haka nan, Ma'aikatar ta shirya ba da wurin zama a Mina kawai ga ƙasashen  da suka kammala shirye-shiryensu a kan lokaci.

IHR ta ce babu yadda za a yi NAHCON ko hukumomin Hajji na jihohi su ba da wata kwangila ba tare da sanin adadi ko kimanin maniyyatan da aka yi wa rijista ba. Wannan kuwa na nuni da irin tasirin da kammala rijista kan kari zai yi yayin Hajjin 2024.

Duk da taƙaitaccen lokacin yin rijista da ake da shi, NAHCON da hukumomin Hajji na jihohi ba su yi wata hoɓɓasa ba wajen faɗakar da maniyyata kan buƙatar soma yin rijista da wuri don gudun fuskantar cikas yayin Hajjin bana.

IHR na cewa abin damuwa ne ainun yadda kawo yanzu jihohi ƙalilan ne suka sanar da fara rijistar Hajji ba tare da la'akari da taƙaitaccen lokaci da ake da shi don yin rijistar ba.

Don haka, muna shawartar hukumomin Hajji na jihohi da su rage yawan kuɗin da ake buƙatar maniyyaci ya fara biya na  Naira miliyan N4.5 da aka ƙayyade saboda hakan na daga dalilan da ke haifar da tafiyar hawainiya game da yin rijistar Hajji a jihohi kamar yadda ake gani.

No comments

Powered by Blogger.