GAYYATAR KORAFI KAN KANFANONIN JIRAGEN YAWO DA ZA SU JAGORANCI HAJJIN BANA
GAYYATAR KORAFI KAN KANFANONIN JIRAGEN YAWO DA ZA SU JAGORANCI HAJJIN BANA
Hukumar Alhazai ya kasa NAHCON, ta jaddada aniyarta na yin adalci ga dukkan masu ruwa da tsaki a harkar aikin hajji a Najeriya. Wannan sanarwa ta biyo bayan korafe korafen da ta samu ne daga jama’a game da sunayen kamfanoni goma da za su jagoranci kamfanonin jiragen yawon da za su dauki maniyyatan aikin hajjin bana.
Hukumar aikin hajji ta kasa ta ce kofarta a bude take ga duk mai korafi a kan kowane kamfani da aka zaba domin tabbatar da ba a yi zaben tumun dare ba a kokarinta na yin adalci da sauke nauyin dake wuyanta.
Dan haka hukumar NAHCON tace duk mutumin ko wata kungiya dake da sahihiyar shaida kan kowane kamfanin da sunansa ke ciki game da rashin cancantarsa da ya kawo mata nan da ranar Juma’a, 3 ga watan Janairun 2025.
Hukumar tace samun kwararan shaidu zai bata damar sake duba wadannan kamfanoni domin zakulo masu nagarta.
Duk wani mai korafi na iya rubuta korafinsa gami da cikakkiyar shaida kai tsaye ga ofishin “The Chairman, National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON)”, nan da ranar Juma’a, 3 ga watan Janeru 2025.
Shugaban hukumar Alhazai ta kasa na tabbatar muku da cewa za a duba dukkan korafe korafen da aka kawo da idon basira tare da yin adalci.
Hukumar NAHCON na neman hadin kan dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da masu kamfanonin jiragen yawo domin cimma burin da suka sa a gaba.
Fatima Sanda Usara,
Assistant Director, Information and Publication,
For Chairman/CEO,
NAHCON
1st January 2025
Fassara:
Suwaiba Ahmed
No comments